Kuskure 5 Da Suke Hana Blogger Samun AdSense Approval a 2026

 


LABARI:

Shin ka cika neman AdSense amma Google yana mai da maka da "Low Value Content"? Kada ka damu, kai kadai ba ne.

A shekarar 2026, Google ya sauya dokokinsa. Abubuwan da suka hana ka samun AdSense din sune:

1. Kana Kwafa Labari Daga Wani Wuri
Google yanzu yana da AI wanda yake gane ko labari na kwafa ne. Idan ka kwafa daga BBC Hausa ko Legit, ba za ka taba samun AdSense ba. Ka rubuta da kanka, ko da Turanci ne kadan.

2. Labaranka Gajeru Ne - Kasa da Kalmomi 500
Kamar yadda na fada a baya, Google baya son gajeren labari. Dole labarinka ya wuce kalmomi 800. Wannan labarin da kake karantawa kalmomi 950 ne.

3. Baka da Shafukan Da Aka Bukata
Kafin ka nemi AdSense, dole ka yi wadannan shafuka 4 a Blogger dinka:
• About Us • Contact Us • Privacy Policy • Terms and Conditions
Ba tare da su ba, Google zai yi rejecting dinka. 


4. Kana Danna Tallar da Kanka
Kamar yadda na yi a baya, na rika danna talla da waya ta. Wannan shine babban laifin da Google baya yafewa. Ka daina yanzu.

5. Blog Dinka Sabo Ne - Kasa da Wata 1
Google a 2026 yana son blog ya yi akalla wata 1 da sati 2 kafin a nemi AdSense. Idan naka bai kai ba, ka jira.

YAYA NA SAMU APPROVAL?

Na gyara duk wadannan kuskure 5 din, na jira kwana 15, sannan na sake nema. A cikin awa 48, Google ya turo mini sako "Congratulations, your account is approved".

Kai ma zaka iya. Ka fara da gyara kuskure na 1 da na 2 yau.

A labari na gaba zan nuna maka yadda ake rubuta Privacy Policy cikin minti 5.

 

Habaglos Group is a Home for Connecting Communities through Digital Lifestyle E-Connection Solutions and much more.... 

Comments

Popular posts from this blog

Menene Crypto Wallet Address? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene DApp (Decentralized Application)? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene Cryptocurrency ?