Sirrin Dalibai a Amurka: Yadda Suke Amfani da AI Don Samun A+ a 2026
LABARIN:
A Amurka, dalibai sun daina kwana suna karatun dare. Suna amfani da AI ne kawai. Amma ba maganar copy da paste bace, akwai dabarar da suke amfani da ita wacce malamai ba sa iya ganowa.
A Habaglos Digital Hub, zamu bude maka sirrin.
1. AI ba ya musu Assignment, yana koya musu ne
Maimakon su ce "Ka min assignment dina", suna cewa "Ka koya min wannan darasin kamar ina da shekara 10". ChatGPT yana bayyana musu har su gane. Hakan ya sa suke samun A+ a jarabawa.
Prompt da suke amfani da shi:
"Explain Quantum Physics to me like I'm a 10 year old Hausa boy who loves football. Use football examples."
### 2. Suna Hada Presentation da Gamma AI a Minti 2
A da, yin PowerPoint yana daukan awa 5. Yanzu, daliban Amurka suna shiga Gamma.app, su rubuta taken, AI ya hada musu presentation mai kyau da hoto da komai a minti 2.
3. Suna Tace Littafi Mai Shafi 300 a Minti 1
Kana da littafi mai shafi 300 da za a yi jarabawa gobe? Kawai ka saka a NotebookLM na Google, zai tace maka shi ya baka summary a shafi daya, kuma ya hada maka tambayoyin da ake iya yi maka a exam.
4. Suna Koyon Turanci da AI
Dalibai a Amurka suna magana da ChatGPT Voice kamar suna magana da Bature. Hakan na taimaka musu su iya Turanci cikin mako 2.
5. Mafi Muhimmanci: AI Detector Bypass
Malaman Amurka suna amfani da AI Detector don gane ko AI ne ya rubuta.
Daliban Amurka sun gano dabarar da za su sa AI ya rubuta kamar mutum: Suna cewa AI din "Ka rubuta kamar dan Adam mai saukin kai, ka saka wasu kura-kurai kadan".
Kammalawa
AI ba ya sa ka zama jahili ba, yana sa ka zama mai wayo ne idan ka iya amfani da shi. Kada ka yi amfani da shi don yaudara, ka yi amfani da shi don ka koyi abu da sauri sau 10.
Shin kai dalibi ne? Wane ne a cikin wadannan kake son in koya maka yadda ake yi? Ka fada a comment.

Comments
Post a Comment