Yadda Mutane Ke Samun $1000 a Wata da AI a Amurka: Hanyoyi 5 da Zaka Iya Farawa Yau
LABARIN:
Shin ka san cewa akwai matasa a Amurka da suke samun sama da $1,000 (Naira Miliyan 1.5) a wata saboda amfani da AI kawai daga gida?
Ba sai ka je Amurka ba, kana nan Azare zaka iya yin wannan aikin kuma a biya ka da Dollar. A Habaglos Digital Hub zamu nuna maka hanyoyi 5 da aka gwada.
1. Rubuta Littafi da AI a Amazon KDP
A Amurka, mutane suna amfani da ChatGPT don rubuta kananan litattafai (eBooks) sannan su sayar a Amazon. AI ne ke rubutawa, kai kuma kudi kake ci.
Kayan aiki:
ChatGPT + Canva AI
Kudin da zaka samu: $200 - $800 a wata.
2. Hada Bidiyo na YouTube ba tare da nuna fuska ba (AI Faceless Channel)
Wannan shine mafi shahara a 2026. Mutane suna amfani da AI don hada muryar mutum (ElevenLabs), su hada hoto (Leonardo AI), sannan su hada bidiyo.
YouTube yana biyan su da Dollar.
Kayan aiki:
CapCut AI + ElevenLabs + ChatGPT
Wannan shine dalilin da ya sa 'yan Amurka suke neman bayani a Google.
3. AI Freelancing a Fiverr da Upwork
Kamfanoni a Amurka suna biyan $50 don a hada musu logo da AI, ko a rubuta musu tallar kasuwanci da AI. Kana iya bude account a Fiverr yau ka fara.
Kayan aiki: Leonardo AI, Looka, Copy.ai
Kudin da zaka samu: $10 - $100 a kowane aiki.
4. Gudanar da Shafin Instagram da AI
Akwai shafukan Instagram a Amurka da suke da followers Miliyan 1 amma ba mutum ne ke gudanarwa ba, AI ne. AI ne ke hada hotuna da rubutu kullum.
Suna samun kudi ta hanyar tallan kamfanoni.
5. AI Voice Over - Ba da Muryar ka ta AI
Idan baka son yin magana, zaka iya bawa AI muryar ka, ta rika yin magana da ita. Kamfanoni suna biyan kudi don wannan a kasuwar Amurka.
Yaya Zaka Fara Yanzu Daga Nigeria?
1. Kana bukatar waya ko kwamfuta da internet kawai.
2. Ka bude asusun Payoneer don karbar Dollar daga Amurka.
3. Ka fara da hanya daya tak. Kada ka rike su biyar lokaci daya. Fara da Fiverr.
Kammalawa
Duniya ta canza. A da sai ka je Amurka ka samu Dollar, yanzu AI ya kawo Amurka gida.
Wane ne daga cikin wadannan hanyoyin 5 kake son in yi maka cikakken bayani a labari na gaba? Ka fada min a comment.
Habaglos Group and Habaglos Digital Hub

Good
ReplyDelete