Gaskiya Mai Daci: Ayyuka 10 da AI Zai Karbe a 2026 da Abinda Zaka Iya Yi
LABARIN:
Tambaya mafi yawa da ake yi a Amurka da duniya a 2026 ita ce: "Shin AI zai karbe aiki na?"
Amsar a takaice: E, wasu ayyuka zai karbe, amma zai kawo wasu sabbi masu kudi mai yawa.
A Habaglos Tech mun bincika rahoton kamfanin Microsoft da Google, ga ayyuka 10 da suke cikin hadari:
Ayyuka 10 da AI Ke Neman Karbe Yanzu:
1. Marubutan Labarai na Copy & Paste: AI yanzu yana rubuta labari a dakika 10, abinda mutum zai yi a awa 3.
2. Masu Shigar da Bayanai (Data Entry): AI yafi mutum sauri da kuskure kadan.
3. Masu Kiran Wayar Tallace-tallace (Telemarketers): Kamfanoni a Amurka sun maye gurbinsu da muryar AI ta ElevenLabs.
4. Masu Zane-zane na Canva na asali: Abokan ciniki yanzu sun fi zuwa Leonardo AI kyauta akan su biya mutum.
5. Masu Fassara na asali (Basic Translators): Google Translate na AI yanzu ya fi mai fassara na yau da kullum.
6. Direbobin Motoci: A California, an fara amfani da motoci marasa direba na Tesla da Waymo.
7. Ma'aikatan Banki na Lissafi: AI yana lissafin kudi da sauri.
8. Malaman Harshe na Farko: Yara a Amurka suna koyan Turanci da AI yanzu.
9. Masu Gyaran Hoto (Photo Editors): Me yasa za a biya mai gyaran hoto alhalin CapCut AI zai yi kyauta?
10. Masu Amsa Wayar Kamfani (Customer Service): Chatbot na AI ne ke amsawa yanzu a kusan dukkanin shafukan Amurka.
To Me Zaka Yi Idan Aikinka Yana Cikin Wannan?
Kada ka ji tsoro. Ga sabbin ayyuka 3 da AI ya kawo wadanda suke biyan $2000 a Amurka:
1. AI Prompt Engineer: Mutumin da ya iya bawa AI umarni daidai. Ana biyansa $50 a awa daya.
2. AI Video Editor: Mutumin da ya iya hada bidiyo da AI ba tare da nuna fuska ba.
3. AI Automation Expert: Mutumin da ya iya hada AI da kasuwanci don ya rika aiki da kansa.
Kammalawa
AI ba zai karbe aikin kowa ba. Zai karbe aikin wanda bai san AI ba ne. Idan ka koyi kayan AI da muka fada a labarin da ya gabata, kai ne zaka maye gurbin wani.
Shin aikinka yana cikin jerin? Ka fada min a comment, zan baka shawara kyauta.

Comments
Post a Comment