Yadda Ake Rubuta Privacy Policy a Blogger Cikin Minti 5 - Ba Sai Kaje Kotuba

 


LABARI:

Shin kana neman AdSense amma baka da Privacy Policy? Kada ka damu, a yau zan nuna maka yadda zaka rubuta ta cikin minti 5 ba tare da lauya ba.

Da yawa daga cikin sabbin masu Blogger suna tunanin dole sai sun je kotu su biya dubu 20 kafin su samu Privacy Policy. Wannan ba gaskiya ba ne a 2026.

MIYECE PRIVACY POLICY?

Privacy Policy takarda ce da take gaya wa Google da mutanen da ke ziyartar blog dinka yadda kake amfani da bayanan su. Kamar cookies, IP address, da email idan sun yi subscribing.

Google baya bawa blog AdSense approval idan babu wannan shafin.

YADDA ZAKA RUBUTA TA CIKIN MINTI 5:

Mataki 1: Je zuwa shafin nan: privacypolicygenerator.org

Mataki 2: Saka sunan blog dinka: Habaglos.com da email dinka.

Mataki 3: Danna Generate, zai baka doguwar takarda da Turanci.

Mataki 4: Kwafa takardar, je Blogger -> Pages -> New Page -> Manna -> Publish.

Shikenan! Ka gama.

WANNAN NE NAWA:

Na yi amfani da wannan hanyar kuma Google ya amince da ita. Ga abin da na saka a tawa:
At Habaglos.com, we respect your privacy. We use cookies to improve your experience and show you relevant ads via Google AdSense. We do not sell your personal data...
Ka iya canza kalmomin kadan don ya dace da naka.

MIYASA WANNAN MUHIMMANCI NE?

Bayan na saka Privacy Policy, About Us, da Contact Us, AdSense approval dina ya zo cikin awa 48. Kafin haka, an yi rejecting dina sau 3.

Idan baka da wadannan shafuka 3, kada ka sake neman AdSense, za a sake rejecting dinka.

A labari na gaba, zan nuna maka yadda ake rubuta About Us mai jan hankali.

Comments

Popular posts from this blog

Menene Crypto Wallet Address? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene DApp (Decentralized Application)? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene Cryptocurrency ?