Dabara Mai Sauki Da Na Yi Amfani Da Ita Na Kara Pageviews Daga 1 Zuwa 3 Akan Kowane Visitor
LABARI:
Ka ga, idan mutum 957 na USA sun shigo, kuma kowannensu ya bude shafi 1 kacal, kana da pageviews 957.
Amma idan kowannensu ya bude shafi 3, kana da pageviews 2,871! Kudin ka zai ninka sau 3 ba tare da ka nemi mutum daya ba.
YADDA NAKEYI:
A karshen kowane labari, kar ka ce "Nagode da karantawa". Kuskure ne.
Ka ce:
KA KARANTA WANNAN:
1. Kalmomi 10 da advertiser ke biyan kudi sosai a kansu (Labari na 13)
2. Yadda na hada labarin Hausa da keyword mai tsada (Labari na 14)
3. Yadda na mayar da mutanen Amurka 957 zuwa kudi (Labari na 15)
Wannan shine Internal Linking. Ka hada labaranka da juna.
ME YASA WANNAN KE AIKI SOSAI GA USA TRAFFIC?
Mutumin Amurka idan ya shigo blog dinka ta Google, kuma ya ga akwai wasu labarai masu ma'ana a kasa, zai danna ya karanta. Kuma kowane dannawa, AdSense yana kara nuna masa sabuwar talla. Damar danna tallan ta karu.
A Blogger, zaka iya yin haka ta atomatik:
Shiga Layout > Main > Add Gadget > Popular Posts ko Related Posts.
Amma mafi kyau, ka rubuta da hannunka a karshen labari kamar yadda na nuna a sama, saboda kana iya saka labarin da kake so ya fi kudi.
AIKI NA YAU:
Dauki labarai 3 na karshe da ka rubuta akan AdSense. Je ka gyara kowannensu, ka saka link na sauran biyun a karshe.
Misali a labari na 15 da ka dora jiya, ka je ka saka link na labari na 13 da 14 a kasa.
Bayan awa 48, duba Stats > Posts. Zaka ga mutane suna bude shafi fiye da daya.
Wannan shine yadda na tashi daga 957 pageviews zuwa 2,000+ ba tare da na nemi sabon mutum ba.
A labari na gaba, zan nuna maka yadda ake amfani da Google Search Console don gano wace kalma ce ta kawo maka USA 957 din, don ka kara rubutu akan ta.

Comments
Post a Comment