Featured post

The 2026 Enterprise Digital Masterclass: AI Architecture, High-Yield Ventures & Global Financial Rails

Image
The 2026 Enterprise Digital Masterclass: AI Architecture, High-Yield Ventures & Global Financial Rails Published by Habaglos Digital Hub | Powered by habaglos.com and Habaglos Group Executive Vision & Leadership: Sani Idris (Abban Habibullah) , Founder & CEO of Habaglos Group Empowering Enterprise Scalability, Advanced AI Engineering, and Global Financial Connectivity — Powered by Habaglos Group Executive Overview As corporate ecosystems across North America, the United Kingdom, and Western Europe transition into advanced digital paradigms, staying competitive demands a comprehensive technological masterclass. Today’s market leaders do not merely adopt software—they engineer robust digital infrastructure, integrate autonomous AI models, and optimize cross-border capital velocity. Spearheaded by **Sani Idris (Abban Habibullah)**, founder of **Habaglos Group** and chief architect of habaglos.com , **H...

Menene Stablecoin? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026



Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum.

Idan kana amfani da cryptocurrency, tabbas ka taɓa jin ana ambaton USDT, USDC, ko DAI. Waɗannan ana kiransu Stablecoins.

Menene Stablecoin? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026)
Gabatarwa: Labarin Malam Musa da Naira

A watan Janairu 2026, Malam Musa dan kasuwa a kasuwar Azare ya ajiye N1,000,000 a banki. A watan Yuli 2026, da ya je kasuwa, wannan N1m ba zai siya masa kaya kamar na Janairu ba - saboda farashin Dala ya tashi daga N1,600 zuwa N1,850. Naira ta fadi.

Abokinsa Alhaji Sani kuma ya canza N1,000,000 nasa zuwa USDT a watan Janairu. Ya siya USDT 625 (a lokacin Dala N1,600). A watan Yuli, ya sayar da USDT 625 din a N1,850 - ya samu N1,156,250. Ya ci riba N156,250 ba tare da ya yi kasuwanci ba, kawai ya kare kudin sa.

Wannan shine Stablecoin.
Stablecoin = Stable (Tsayayye) + Coin (Kudi)

Ma'ana: Kudin crypto ne wanda farashinsa ya tsaya, baya hauwa baya faduwa kamar Bitcoin.

Bitcoin yau $110,000, gobe $90,000 - yana faduwa yana tashi. Amma USDT yau $1, gobe $1, jibi $1 - ya tsaya.

Yaya Ake Hada Stablecoin? - Misali Mai Sauki

Ka yi tunanin kana da akwati. A cikin akwati, ka saka Dala $1,000 na gaske a banki a Amurka. Sannan ka buga takardun biredi guda 1,000 ka rubuta musu "Wannan takarda tana daidai da Dala 1 a cikin akwati". Kowa ya amince da takardunka saboda ya san akwatin yana da Dala.

USDT haka yake. Kamfanin Tether yana da Dala biliyoyi a banki. Sannan ya kirkiro USDT biliyoyi a Blockchain. Kowane USDT 1 = Dala 1 na gaske a bankin Tether. Idan kaje da USDT 1,000, zasu baka Dala 1,000 (a ka'ida).

Ire-iren Stablecoin 4 da Muke Amfani da su a Najeriya 2026

1. USDT (Tether) - Sarkin Kasuwa

Abin Kwatance USDT (Tether) USDC (Circle)
Farashi $1 $1
Fee (TRC20) $1 (Mafi arha) $1.20
Amintacce 90% - Ba sa fitar da rahoton banki sosai 99% - Suna fitar da rahoton kowane wata
A Najeriya Kowa ya yarda da shi, P2P yafi yawa Sabo, amma yana girma
Shawara Ka yi amfani da shi don kasuwanci na yau da kullum Ka yi amfani da shi don ajiya mai tsawo

Mafi shahara a Najeriya - 80% na kasuwancin crypto a Najeriya USDT ne. • Kowane USDT = $1 • Yana aiki a kan Tron (TRC20), Ethereum, da Solana. • Mafi arha wajen tura kudi. • Shawara: Ka fara da wannan. 
2. USDC (USD Coin) - Dan Amurka Mai Gaskiya
• Kamfanin Circle na Amurka ne ke da shi, kuma gwamnatin Amurka tana sa ido a kansa. • Mafi aminci fiye da USDT, saboda kowane wata suna fitar da rahoton banki. • A 2026, yawancin manyan kasuwanni kamar Amazon suna karbar USDC. • Farashinsa ma $1. 
3. DAI - Stablecoin na Gaskiya (Decentralized)
• Wannan ba banki ke da shi ba, code ne ke da shi. • Ana hada shi ne da saka Ethereum a matsayin jingina. • Mafi wahalar gane wa, amma babu gwamnati da za ta iya rufe shi. 
4. cNGN da eNaira Stablecoin - Na Najeriya
• A 2025, wasu kamfanonin Najeriya sun kirkiro cNGN - Stablecoin da ke daidai da Naira 1. • Amma har yanzu mutane ba su yarda da shi ba sosai, domin Naira kanta tana faduwa. Me zai sa ka ajiye stablecoin na Naira idan Naira tana faduwa? • eNaira ma stablecoin ne, amma na CBN ne, kuma yana da matsala wajen amfani. 
Don haka a Arewa, muna amfani da USDT da USDC ne kawai.

Me ya sa Mutane a Arewa Suke Son Stablecoin Fiye da Bitcoin? 

- Dalilai 5
1. Kare Naira daga faduwa (Hedging):
Kamar labarin Malam Musa. Idan kana da N500k da baka son ya fadi, ka canza shi zuwa USDT. Idan Dala ya tashi, naka ma ya tashi.

2. Kasuwanci na Kasa da Kasa:
Idan kana sayen kaya daga China a kasuwar Kano, ba sai ka je banki ka bi layi ba. Ka tura USDT ga dan China cikin minti 2, fee $1. Banki zai karbe ka $30 fee kuma zai dauki kwana 3.

3. Ajiya ba tare da Banki ba:
Wasu matasa a Azare ba su da BVN, ba sa iya bude account. Amma suna da Trust Wallet da USDT 100. Wannan ajiyarsu ce.

4. Biyan Albashi da Freelancing:
Da yawa daga cikin yaran da ke aiki a Upwork da Fiverr a Bauchi, ana biyan su da USDT saboda saurin sa. Idan an biya su $100, ya shigo wallet dinsu kai tsaye.

5. Bashi da Lamuni (DeFi):
A 2026, zaka iya saka USDT dinka a wasu apps kamar Binance Earn, su ba ka riba 8% a shekara. Wannan ya fi ribar banki (wanda 5% ne).

Hadarin Stablecoin - Kada Ka Rufe Ido

Duk da dadinsa, akwai hadari.

1. Hadarin Kamfani (De-pegging):
Idan kamfanin Tether ya yi karyar cewa ba shi da isassun Dala a banki, USDT zai iya faduwa daga $1 zuwa $0.90. Wannan ya taba faruwa a 2022 da wani stablecoin mai suna TerraUST - mutane sun rasa biliyoyi.

Amma USDT da USDC har yanzu suna da karfi a 2026.

2. Gwamnati na iya rufe shi:
Gwamnatin Amurka na iya cewa Tether ya rufe address dinka idan tana zargin ka da laifi. Wannan ya faru ga wasu 'yan damfara.

3. Kuskuren Network:
Kamar yadda na fada a darasin Send & Receive, idan ka tura USDT TRC20 zuwa ERC20, ya bace.

Yadda Zaka Siya da Ajiye Stablecoin Lafiya - Matakai 3

Mataki 1: Siya a Waje Mai Amintacce
Kada ka siya a hannun mutum a WhatsApp. Ka siya a Yellow Card ko Busha. Suna da USDT na gaske.

Mataki 2: Tura zuwa Wallet Dinka (Ba a Bar shi a Exchange ba)
Idan ka siya USDT 200 a Yellow Card, ka tura zuwa Trust Wallet. Domin idan Yellow Card ta rufe gobe (Allah ya kiyaye), kudin ka yana nan a wallet dinka.

Mataki 3: Ka Rike Seed Phrase Dinka
Kamar yadda na fada, 12 kalmomin nan sune kudin ka. Ka rubuta a takarda ka boye a gida. Kada ka dauka hoto a waya - idan an sace wayarka, an sace kudin.

USDT vs USDC - Wanne ne Mafi Kyau a Gare ka a 2026? 

Nawa na Rike:
Ni da kaina, ina rike 70% USDT da 30% USDC. USDT don kasuwanci, USDC don ajiya mai tsawo.

Kammalawa.
Stablecoin shine gada tsakanin Naira da Dala. Ba ya tashi kamar Bitcoin, amma yana kare kudin ka daga faduwa. Ga dan Arewa mai kasuwanci ko mai neman ya kare N10,000 dinsa, Stablecoin shine mafi kyau.

A darasi na gaba, zan koya maka Yadda Ake Samun Riba da Stablecoin (Staking) ba tare da ka siyar ba - yadda zaka saka USDT 100 ya rika baka $8 a shekara. 

Stablecoin wani nau'in cryptocurrency ne da aka ƙera domin farashinsa ya kasance kusan daidai da kuɗin ƙasa kamar Dalar Amurka (USD).

Misali:

A. 1 USDT ≈ $1

B. 1 USDC ≈ $1

Saboda haka, Stablecoin ba ya yawan tashi ko faÉ—uwa kamar Bitcoin ko Ethereum.

Amfanin Stablecoin

Ajiye kuÉ—i ba tare da tsananin canjin farashi ba.

Sauƙin aika kuɗi tsakanin wallets.

Yin ciniki (trading) cikin sauƙi.

Kare riba lokacin da kasuwa ta faÉ—i.

Mafi Shahararrun Stablecoins

1. USDT (Tether)

2. USDC (USD Coin)

3. DAI

4. FDUSD

Habaglos Info-Tech in Collaboration with Internet Ikon Allah Global Links and E-Connection Solutions...!!!

Comments

Popular posts from this blog

Menene Cryptocurrency ?

Menene DApp (Decentralized Application)? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)

Menene Crypto Wallet Address? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)