Featured post
Menene Web3? Cikakken Bayani Cikin Hausa (2026 Guide)
- Get link
- X
- Other Apps
Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu Alaikum.
Menene Web3? Bayani Mai Sauki Cikin Hausa.
Ka tuna lokacin da Facebook yake rufe account din mutane ba gaira ba dalili? Ko lokacin da banki ya rufe maka account saboda ka karbi kudi daga waje?
Wannan matsalar ta Web2 ce - Kamfanoni ne ke da iko da komai.
Web3 ya zo don ya dawo da iko hannun ka.
Web3 = Sabon Internet inda Kai ne Mai Mallakar Bayananka da Kudinka
Tarihin Internet a Takaice: Web1 -> Web2 -> Web3
| Web1 (1990-2004) | Web2 (2004-2024) | Web3 (2025-2030) |
|---|---|---|
| Read Only Karatu kawai |
Read + Write Karatu da Rubutu |
Read + Write + Own Karatu, Rubutu, da Mallaka |
| Static Websites | Facebook, YouTube, TikTok | Blockchain, Crypto, NFTs |
| Kamfani ne ke wallafa | Kai ke wallafa, Kamfani ke da ikon bayanan ka | Kai ke wallafa, KAI ne mai ikon bayanan ka |
| Babu login | Login da Email/Password | Login da Wallet (MetaMask) |
Manyan Ginshikan Web3 (5 Pillars)
- 1. Blockchain: Littafin da babu mai iya gogewa - Gidauniyar Web3
- 2. Cryptocurrency (USDT, ETH, SOL): Kudin Web3 - Ba sai banki ba
- 3. Smart Contracts: Kwangilolin da ke aiwatar da kansu - Maye gurbin lauya da banki
- 4. NFTs: Takardar mallaka ta digital - Shaidar cewa kai ne mai abu
- 5. DAOs (Decentralized Autonomous Organization): Kamfani ba tare da shugaba ba - Al'umma ne ke yanke shawara ta hanyar kuri'a a Blockchain
Misalai na Web2 vs Web3 a Najeriya
- Facebook na iya rufe page dinka mai followers 100k
- GTBank na iya rufe account dinka
- YouTube na iya cinye monetization dinka
- Bayanan ka Facebook ke sayarwa
- Babu wanda zai iya rufe wallet dinka
- Kana tura USDT kai tsaye, babu banki a tsakiya
- Bidiyonka na a IPFS, babu mai iya gogewa
- Kai ne mai bayanan ka, zaka iya sayar da su ka samu kudi
Me yasa Web3 ke da Muhimmanci ga Dan Najeriya a 2026?
1. Samun Dala ba tare da Banki ba: A Web3 zaka iya aiki a kamfanin waje ka karbi albashi da USDT kai tsaye a wallet dinka, ba sai Payoneer ko domiciliary account ba.
2. Mallakar Abin da ka Kirkira: Idan ka wallafa waka a Audius (Web3 Spotify), wakar taka ce 100%, ba Spotify zai ci 70% ba.
3. Gudun Haramcin CBN: Bayan dokar CBN ta 2021, Web3 ya bawa 'yan Najeriya damar ci gaba da kasuwancin crypto ba tare da banki ba ta hanyar P2P da DeFi.
4. Micro SaaS & Aiki: Yanzu zaka iya gina karamin app a kan Ethereum da ke baka $500 a wata ta atomatik - Wannan shine Micro SaaS na Web3.
Yadda Ake Shiga Web3 daga Azare / Najeriya (Mataki 3)
- Bude Wallet: Zazzage MetaMask ko Phantom - Wannan shine ID dinka na Web3, ya maye gurbin Email.
- Sami Crypto: Sayi kadan na ETH ko SOL ta Binance P2P da Naira - Wannan zai zama kudin Data na Web3.
- Shiga DApps: Shiga Uniswap.org (musanya kudi), OpenSea.io (NFTs), ko Mirror.xyz (rubutu) - Ka hade wallet dinka ka fara amfani.
Web1 = Kamfani ne ya gina Internet.
Web2 = Kai da Kamfani kuka gina shi, amma Kamfani ne ya mallake shi.
Web3 = Kai ne zaka mallaki Internet din gobe.
A 2026, wanda bai shiga Web3 ba, zai zama kamar wanda bai shiga Facebook ba a 2010.
1. 👉 Menene NFT? Cikakken Bayani Hausa 2026
2. 👉 Menene Smart Contract? Cikakken Bayani
3. 👉 Menene Bitcoin? Cikakken Bayani
4. 👉 Yadda Ake Siyan Crypto Cikin Tsaro Nigeria
Idan kana yawan jin ana maganar Web3, wataƙila kana tambayar kanka: Mene ne Web3?
Web3 sabon salo ne na amfani da intanet wanda yake amfani da blockchain, cryptocurrency, da wallet domin ba masu amfani cikakken iko akan bayanansu da dukiyoyinsu.
Menene Web3?
Internet da masu amfani ne suka mallake shi, ba manyan kamfanoni ba, ta amfani da Blockchain, Smart Contract, da Cryptocurrency.
Web3 shi ne sabon ƙarni na intanet wanda aka gina akan fasahar blockchain.
A Web3, kai ne kake da iko akan bayananka da kuÉ—inka, ba kamar tsohon tsarin da manyan kamfanoni suke da cikakken iko ba.
1. Blockchain (Littafin da ba a gogewa):
• Duk bayanai suna nan a fili, ba wanda zai iya canza su.
2. Smart Contract (Kwantiragi mai hankali):
• Wannan ne muka yi bayani a baya. Shi ne dokar da ke tafiyar da Web3 ba tare da dan tsakani ba.
3. Cryptocurrency / Token (Kudin Web3):
• Kudin da ake biyan juna kai tsaye. Misali ETH, SOL. Misalai 4 na Web3 da za ka gane yanzu:
1. Blogger na yau (Web2) vs Blogger na Web3:
• Web2 (Yanzu): Ka rubuta a Blogger. Google ne ke mallakar blog din. Idan Google ya ce ya rufe Blogger gobe, blog dinka 166 sun tafi. • Web3 (Nan gaba): Ka rubuta a Mirror. Rubutun naka yana blockchain. Ko Mirror ya rufe, rubutun naka yana nan, kuma masu karatu na iya ci gaba da biyan ka da ETH kai tsaye.
2. Banki vs DeFi (Web3 Bank):
• Banki (Web2): Ka ajiye N100k, banki ya baka 4% riba, amma ya ci 10% charges. • DeFi - Aave (Web3): Ka kulle $1000 USDC a smart contract, ka samu 8.9% riba kai tsaye, babu charges na boye. Kamar yadda muka fada a Altcoin.
3. Facebook vs Lens Protocol (Web3 Facebook):
• Facebook: Followers 10k dinka na Facebook ne. Idan aka block account dinka, sun tafi. • Lens (Web3): Followers dinka suna wallet dinka. Ko an block ka a wani app, zaka iya koma wani app da followers dinka duka.
4. Wasanni:
• Web2 Game (Free Fire): Ka sayi skin N5k, idan game ya rufe, kudinka sun tafi. • Web3 Game (Axie): Skin dinka NFT ne, naka ne. Zaka iya sayar da shi ga wani da ETH.
Bambancin Web1, Web2 da Web3
Web1
Karanta bayanai kawai.
Ba a cika yin mu'amala ba.
Web2
Ana karantawa kuma ana rubutawa.
Social Media kamar Facebook, X (Twitter), Instagram da YouTube sun shahara.
Kamfanoni ne ke sarrafa bayanai.
Web3
Ana amfani da blockchain.
Kai ne mamallakin bayananka.
Ana amfani da Wallet wajen shiga Apps.
Ana amfani da Cryptocurrency wajen biyan kuÉ—i.
Muhimman Abubuwan Web3
Blockchain
Wallet
Smart Contracts
DApps (Decentralized Applications)
DeFi
NFTs
DAOs
Fa'idodin Web3
✅ Karin tsaro.
✅ Kai ne mamallakin bayananka.
✅ Babu buĆ™atar banki wajen wasu mu'amaloli.
✅ SauĆ™in amfani da cryptocurrency.
✅ Sabbin damar samun kuÉ—i ta hanyar Web3.
Matsalolin Web3
Sabuwar fasaha ce.
Akwai masu damfara.
Idan ka rasa Seed Phrase, za ka iya rasa wallet É—inka.
Wasu Apps suna da wahalar amfani ga masu farawa.
Misalan Web3 Apps.
Uniswap
OpenSea
Aave
MetaMask
Trust Wallet
Kammalawa.
Web3 yana canza yadda mutane ke amfani da intanet ta hanyar ba su iko akan bayanansu da dukiyoyinsu. Yana amfani da blockchain domin samar da tsaro da gaskiya a mu'amaloli.
Internet Ikon Allah Global Links and E-Connection Solutions in Collaboration with Habaglos Info-Tech
- Get link
- X
- Other Apps

Comments
Post a Comment