Yadda Na Fara YouTube Channel Ba Tare da Nuna Fuska Ba kuma Na Samu $500 da AI
LABARIN:
Shin ka san akwai YouTubers a Amurka da suke da subscribers Miliyan 1 amma har yanzu ba a taba ganin fuskarsu ba? Sirrin su shine AI.
A Habaglos, zan koya maka yadda zaka fara irin wannan channel din a kwana 3 kacal.
Mataki 1: Ka Zabi Taken da Amurka Ke So (Niche)
Kada ka zabi labaran gida kawai. Ka zabi wanda Amurka ke biya mai yawa. Ga 3 mafi kudi:
1. AI Stories / Scary Stories: Labarai masu ban tsoro.
2. History Facts: Abubuwan tarihi da aka manta.
3. Finance Tips: Yadda ake tara kudi.
Wadannan ne suke biyan $10 akan kallo 1000 a Amurka.
Mataki 2: Ka Rubuta Labari da ChatGPT
Ka ce masa:
"Write me a 5-minute scary story about a house in Texas that no one can enter.
Make it very suspenseful."
Zai baka labari a dakika 10.
Mataki 3:
Ka Mayar da Labarin Murya da ElevenLabs
Ka kwafa labarin ka saka a ElevenLabs.io, ka zabi muryar wani Bature mai zurfi. Zai karanta maka labarin kamar mutum 100%.
Mataki 4:
Ka Hada Bidiyo da CapCut AI
Ka bude CapCut, ka saka muryar, ka danna "Auto Generate Video". CapCut zai saka maka hotuna da bidiyoyi masu dacewa da labarin da kansa.
Mataki 5:
Ka Dora a YouTube
Ka saka taken mai jan hankali: "The Texas House No One Dares to Enter at Night"
Shikenan. Ba ka nuna fuska, ba ka yi magana da bakinka, amma kana da bidiyo.
Nawa Zaka Samu?
YouTuber daya a Amurka mai suna "Mr. Nightmare" yana samun $15,000 a wata da irin wannan. Kai kuma zaka iya fara samun $500 na farko idan ka dora bidiyo 20.
Kammalawa
Duniyar YouTube ta canza. Ba sai kana da kyakykyawar fuska ko murya mai dadi ba. Sai kana da wayo da AI.
Gobe zan kawo maka jerin Prompts 10 da zaka iya amfani da su don fara channel dinka.
Shin kana son in aiko maka da bidiyo na yadda ake yi ne? Ka rubuta "E" a comment.

Comments
Post a Comment